Tuesday, 19 July 2016

Anya Lionel Messi Zai Kai Labarin Kuwa ?


Hukumar kwallon kafa ta duniya, watau FIFA, ta bayyana sunayen mutane goma da suka fito daga kungiyoyin na nahiyoyi daban daban wadanda suke kan gaba wajen neman zama zakar kwallon kafa na duniya watau (World Best Player) na shekarar 2015/2016.

Wadannan ‘yan wasa sune Gareth Bale dan kasar Wales, mai taka leda a Real Madrid, sai Buffon dan kasar Italiya mai wasa a Juventus, Antoine Griezman, mai bugawa Atletico Madrid, dan kasar Faransa, Toni Kroos dan kasar Jamus mai yin wasa a Real Madrid, da Lionel Messi, mai rike da kanbin a yanzu dan kasar Argentina mai murza leda a Barcelona.

Sauran sun hada da Thomas Mueller dan kasar Jamus kuma dan wasan Bayern Munich, ta kasar Jamus, sai Manuel Neuer, shima dan kasar Jamus kuma dan wasan Bayern Munich, sai Pepe dan kasar Portugal Mai takawa Real Madrid leda, Cristiano Ronaldo,dan kasat Portugal, dan wasan Real Madrid da Luis Suarezdan kasar Uruguay dan wasan kungoyar Barcelona suma suna cikin masu neman wannan kanbi.

Hukumar tace ranar 25, ga watan Agustan wannan shekarar zata sanar da sunan wanda ya sami nasara zama zaka kuma gwarzon kwallon kafa na shekara 2015/2016.

Sai dai a duk sunayen da hukumar kwallon kafa ta duniya watau FIFA, ta fitar babu sunan daya daga cikin masu taka leda a kasar Ingila, wanda wannan ke nuna koma baya a harkar primiyar Ingila.

Blogger
Disqus
Pilih Sistem Komentar Yang Anda Sukai

No comments