Sunday, 5 November 2017

BIBIYATA AKEYI 3

BIBIYATA AKEYI          

Bismillahirahmanirrahim

Writing by
             Zaynab Bawa(z33iiyyb3rw3r )

Page 3
*
            DUBAI

Wani tangameman gida nahango, wanda fadin girmansama tsayawa bata bakine, kyawunsa kuwa kokadan baya misaltuwa domin bansan dawani yare zanmuku bayanin da har zakugane kyau tsaruwar wannan gida ba, hatta tsaron gidan ma, sojojine masu tsaran gidan sunza gayeshi , tako wani sako da lungu gaba da baya,
Azatona tunda kasar larabawa ne nadauka sojajin larabawa zangani amma inah zancen yasha bam bam,

Sojojine kala kala wanda kowace kasa sanda suka bada gudumawa wajen kare lafiyar wannan bawa nasa, kowani soja yana sanyene da kakin kasarsu sojojine bila adadin wanda irga yawansuma bamai yiwuwa bane,

Mamaki da alja'abi suncikani waishin waye wannan dan adam dinda ake gadin rayuwarsa haka. ko sucurities  dasuke gidan shugaban kasa basukai natsaron wannan bawan Allah  yawaba,

MAJOR GENERAL (MG) Abudullahi kukeji daya tamkarda dubu, gwarzon namiji wanda kallonsa kadae ke razana makiyah, ba country dinsa ba kadai
 hatta da sauran kasashen sunaji dashi shiyasa suke bada gudumawa wajen kare lafiyarsa, domin shi mai sadaukarwa al'ummah rai da lafiyarsa ne,

Zaune yake kankujerar tangameman falonsa kafanshi daya akan daya ya jingina da kujera  karkada kafansa yakeyi ahankali cikin nutsuwah da solon birgewa,

Farineh tass kyakkyawan gaske wanda kana kollonsa dakaga kamanninsa da larabawa dogo neh sambal mai faffadan kirji, gwarzon namiji, subhanallah kyawun wannan bawan Allah, abin ba'acewa komai, saidaai hamdala. idanuwansa farare tass kwayar cikin kuwa bakikirin shape dinsu oval ne masu kyawun gaske, gashin kansa bakine sidik, with his cute pink lips, OMG he's damn cute, i don't even knw how to describe him, he's so muah👄

Rurinda wayarsa tadaukane yasashi bude idoh ahankali cikin nutsuwa daukan wayar yayi tareda karata akunnensa.

Amsa sallama yayi sannan  yayi hade dayin murmushi subhanallah kyawunsa baisake bayyana ba saida both side na face dinsa suka lotsa (beauty point)
Abin al'jabin baizoba sanda yafara magana da hausa wadda hakan ba karamin abin mamaki bane
Amsawa yayi da toh abba ammafa akwae abinda nakeyi wadda haryanxu bankarasaba yana maganane cikin natsuwa abba ba halin tafowane cewarsa dadahali danazo cikin week dinnan saboda nima nayi kewarka ina bukatar ganinka to
Call u later baejira mai za'aceba kit yakashe wayan

Wata nauyayyar ajiyar zuciya yasauke kokadan bayason abinda zaisa yaje gida yanxu

Danbaxai iya jira lokaci yacika kafin ya cika kudurinsaba yafi masa sauki yajira lokacin kafin yashiga kasarsa tahaihuwa

Karar saukowar takalmintane yakatse masa tunanin dayakeyi
Wata farar matace wacce bazatafi shekaru hamsin da biyar ba kana kallonta ko tantama bbu dakasan itace mahaifiyar MG Abudullahi balarabiyace
Kyakkyawar gaske
Ko banfada ba kunsan yanayin yanda kyawun larabawan Dubai yake
Karasowa tayi dauke da murmushin dake kara fitoda kamanninsu da MG Abudullahi zama tayi kusa dashi tadafa shi sannan tafara magana cikin harshen larabci

Meyake dmunka haka naga gabaki daya yanayinka yachanja lokuta da dama nakan fada maka kacire wata fargaba bbu wata wacce xatasamu miji kamarka tace bataso kanada kyau da mulki da kuma dukiya bbu wata mahalukiayar da zata kika

Shiru yayi nayan wasu dakika sannan yace ummee bana so asoni dankyawu na ko kudi kowani mulki danake tattare dashi

Mutane dayawa bawae sunasona bane wasu tsoro nane yakesawa sununamin so wasu kuma dan dukiya da mulki yasa suke sona bawai har zuciyah ba wani zafaffen huci yafitar yakara damke hannun ummi dayake rike dashi ummee tajawoshi jikinta ahankali tafara shafa kansa batareda tace komaiba

Aranta kuma tanace Allah kasaukakawa wannan bawa naka wannan jarabawar da ya tsinci kanshi aciki tana tausayin danta ace yakamu dasan wanda basumasan ko tana existing ba

================

Yauma kamar kullum shiri tayi tsab nazuwa makaranta doguwar rigane ajikinta ta yane kanta da gyalen rigar wadda hakan yafito da sihirtaccen kyawunta wanda ba lokaci daya kake kollonta kagano wannan kyawunba

Jakarta ta zara direct dakin babansu tanufa dasallama tashiga sanda ya amsa sannan tashiga tagaisheshi ya amsa da fara'arsa kinfuto kenen eh baba yanxu zanwuce dari biyar yaciro yabata godiya tayi masa sannan tatashi yafibata dakyakkyawar addu'a wadda yakamata duk wani mahaifi yayiwa diyarsa lokacin da zataje wani waje nadaban

Fitowa tayi zuwa bakin titi domin samun abun dazatahau tawuce makaranta duk da chanja mata dasukayi hakan baihanata fahimtar suwaye acikin motar ba adaidata tayi saurin tsara tahau batayi mamakin binta da motar takeyiba har zuwa makaranta sannan ta sallami mai adaidata tayi cikin school din

Sanda suka shiga lectures 80:30 tayi basu suka fitaba basai 11:30 dayake 3hour lectures ne sunafita taji wani irin........

To be continue

Ur's
     Z33yyb3rw3r

BIBIYATA AKEYI 2

BIBIYATA AKEYI          

Bismillahirahmanirrahim

Writing by
                _Zaynab Bawa (z33iiyyb3rw3r)_
         

Page 2
*
Gani tayi kamarda inuwar mutum akanta agigice tafarka lokaci daya kuma tasauke ajiyar zuciya ganin mama dake tsaye akanta,

Sunkuyar da kanta tayi sannan tace sannu dashigowa Mama batareda ta amsa taba tasamu waje tazauna sannan tace *hanna* ta dago takalleta cikin sanyin murya tace na'am mama,

Meyake damunki kifadamin dan banasan kallonki cikin damuwa murmushin yake ta kirkiro sannan tace bbu komaifa mama mekika Gani shiru mama tayi tazuba mata ido tana nazarin yanayinta ta kunsan uwa da danta koyaya dah yakai da boye damuwarsa takan gane yana cikin damuwa

*hanna* sunanta da mama takira ne yasata dago kanta daga sunkuyen da take sannan tace na'am mama tadaura da cewa nimahaifiyar kice kina tunani idan baki fadamun damuwarkiba akwae wanda yacancanta kifadawa bayanni

Murmushin yake takara kwakulowa sannan tace Allah mama bbu komai kainane yakemin ciwo kuma gashi samester yazo tsakiya karatu yafara zafi

To Allah yasauwake kisha magani saikihuta mama tafadi hakane bawae danta yarda cewa yartata bata da wata damuwa ba, kuma bawae dan tanada tabbacin datasha maganinba

Mama nafita tasauke ajiyan zuciya tareda jawo alqur'ani taci gaba da karantawa nantake taji kashi tamanin daga cikin dari na damuwarta ya gushe damuwarta ta batafi saura kalilanba

Rufe qur'anin tayi sannan tanade pray mate din cikin natsuwa tanufi kofar       Fita daga dakin

================

katafaran masarautace mai girman gaske
Wanda ko bantsaya muku bayaniba kunsan yanayin girman masarautar kano dan tana daya daga cikin masarautu masu girman gaske
A wannan kasa tamu masarautace mai yawon jama'a

Da dumbin alkhaire atattare acikinta wanda kuma tasamu adali jajirtaccen sarki dattijon  arziki mai farar aniya

*Sarki*Abdulaziz lamido

Wata mata nahango zaune akatafaren falon sarki wanda yasha kayan alatu dana more rayuwa matar dake zaune afalon kana kallonta koba'afada ba kasan itace matar sarki domin ko daga yanayin kayan dayake jikintama zainuna hakan balle azo zuwa yanayin fatar jikinta

Dukda dai bawata walwala atare da ita amma hakan baihana kyawun fatarta futowa kallo daya daka mata kagane damuwar dake tattare afuskarta

Ahankali tasa gefen gyalenta tamatso kwalla sannan tace mai martaba badai kanaso kagwadamin bani na haifeshiba shiyasa kaki amincewa da kudurina amma kasan yanda nake sansa araina koh yayan dana haifa bana sonsu haka

Kasan yadda nake jinsa araina kuwa  tafada cikin muryar kuka inajin ciwo acewae shekara 35 amma haryanxu yagagara yin aure kuma munzuba masa idoh muna kallonsa

Nifa wannan yarinyar daya damu da ita atunanina aljanace ba mutum ba, mai martaba yakura mata ido kawae domin bayaso yatsaida ita saita dasa aya

Sannan taci gabada cewa tayaya xa'ace shekara tara kenan kullum zancensa mutum daya bamusanta bamutaba kallontaba

Mai martaba baza'aduba wannan zance ba idan da'abi shawarata atara malamai kawae suyita masa rokon Allah har adace wannan aljana tarabu dashi

Gyaran murya mai martaba yayi sannan yace bawae naki tatakiba amma yakamata mujira harsai shekatunda ya eba mana suncika kafin muyanke masa hukunci

Ainida ba se anjira ba dan wannan ba mutum bace ga yar uwarsa intisar aisai ahadasu

Kilishi Kilishi Kilishi mai martaba yakira sunanta tareda hadaerai sannan yace

Nafada miki alkawari na dauka zanbarshi yacika wannan lokacinda ya eba donhaka banasan sake jin tashin maganar nan

Toh tace amma bawae dan ranta yasoba sannan tatashi tawuce zuwa shashinta

Tana Fita fadawa sukafara kwasan gaisuwa amma ko kollonsu batayiba tawuce dayake Kilishi Allah yayita mace mai girman kai dakuma nuna isah

================

Zaman cikin gidanne yasoma gagararta domin sai habaice habaice kawae akeyi

Koda Mama taji abinda Su Amma sukeyi hakan baisa tatanka musu ba dan inda sabo tasaba kuma Allah yayita mace mai hakuri wanda gane fushinta abune mai wuya

Juyarda kanta tayi wajan inna kaltu sukacigaba da aikinsu domin yau itace mai girki domin bata taba bari mai aiki tayi ma mijinta abinci itata keyin kayanta

*Hanna* tashi tayi tayi da niyar shiga daki Hafsat da rabi'ah wanda suke yayu a wajanta ne suka tafa tareda shekewa da dariya Hafsat tace dama wasukam Ai saidai Zaman daki domin ba mashin shini suka kara tafawa yoh saima kunbata bakinkune kewar amma aixaman daki yanxu akaafarashi

Zuruf *hanna* tashige daki domin itama kanta abunyana damunta wani irin bakin jinine dani tafada tareda fashewa da matsanancin kuka

Amma yau tasamowa kanta amsar tambaya tada dade tana addabarta aranta, aljanine dagaske ya aureta tunda da kunnan ta taji bawani bane yajimata

Toh sukuma wayannnan masu *bibiyarata* suwaye shin ko suma aljanune??? ta tambayi kanta

Wannan tambayarne haryanxu takasa samun amsar ta kuma batasan wazata nema ya amsa mataba

Saidai takudirta aranta bawanda zaiji wannan zancen
Ai idan aljani yafi karfinta Toh itama akwae wanda zata kai karansu wajan sa

Tadauki alkawarin yin tsayiwar dare tahana idanta barci harsai Allah yamata sakayya da wayannan azzalumai masu BIBIYAR rayuwar ta.

Shin wae waye itah wannan hanna?????

Shikuma wannan wanda iyayansa suke tunanin aljana ta aureshi wayeshi????              

To be continue

Ur's
     Z33yyb3rw3r

Wednesday, 1 November 2017

BIBIYATA AKEYI 1

. BIBIYATA AKEYI        

Bismillahirahmanirrahim

Writing by
            _Zaynab Bawa (z33iiyyb3rw3r)_

Page 1

Zaune take acikin wajan amma hankalinta baya jikinta domin kana kallanta kasan tana cikin matsananciyar damuwa wanda hakan yagaza boyuwa sanda yanuna akyakyawar fuskarta,

 Tunani take acikin zuciyarta shin ko tajene tasamesu taji dalilin wannan *bibiya* da takura dasuke mata ne, atake wata zuciyar tayi saurin gargadarta domin batasan mugaye bane,

Amma aida mugaye ne dasun dade da cutar dake, wata zuciyar tace da ita. Mtswww taja wani dan siririn tsaki, ni wallahi tsoronsuma nakeji tafada cikin muryar kuka tareda kifa kanta ajikn table dinda yake gabanta.

Tosu wayannan mutanen suwaye?? mesuke nema awajanta??? Wani laifin tamusu dasuke *bibiyar*rayuwarta?? dataga dai bata dayadda datasamu amsar tambayoyinta kawai tamike tare da zarar jakarta tayi hanyan fita daga restuarant din dake cikin school din zuwa hall na lectures dinsu tana kallo daya yayiwa daya magana da alamu nuna masa ita yayi akan tatashi subita koda taga haka wuff tafice daga cikin wajan batareda datsaya biyan kudiba dan damuwa bata barta tayi ordering  komaiba

Koda tafita tayi noticing ana binta amma hakan be daga mata hankalinta dan abunyafara binjiknta direct hall dinda zasuyi lectures tawuce tasamu har malamin sunshiga sa'arta daya bame tsanani bane yasa tayi saurin shiga tasamu gefen kawarta amira tazauna

Amira rada tamata akunne ke inata kiran phone dinki ina kika shiga kikabari phone anata kira banza ainaso kiyi missing attendance,

Gabaki daya wannan surutun da amira takeyi batasan atakure dakeba kawae tatashi tacanja wajen zama tace kici kanki

Ana tashi kuwa ko takan amira batayi ba tafice dama shine last lecture dinsu na ranan,                kodatafita batayi mamakin ganinsu ba don tasan za'a rina (wae miji ya saki mata ubansa yaje zauranci)
Fita tayi tawuce gida koda tana keke napep ma haka taga suna binta sanda tazo dab shiga gida kafin suka juya,

Tana shiga gida tasauke wata nauyayyan ajiyan zuciyarta,
Da sallama tashiga tasamu babansu harya dawo tatsuguna aladabce tamasa sannu da hutawa ya amsa cikin sakin fuska sannan tatashi zata tafi harta fara tafiya naji yace, *hanna*

*Hanna*ni unknown nakara maimata sunan araina nace amma sunan yayi saurin juyowa tayi  cikin ladabi da nitsuwa tace na'am baba yace idankin shiga ciki kyakiramin mamanki toh tace tareda juyawa

Tacigaba da tafiya cikin nutsuwa giftawa tajeyi taji wani zancen daya hargitsa mata Tunani yakara gigitata tare da tsundumata cikin damuwa kunnenta takara kawowa kofar dakin taji hajiyah lami wacce suke kira da Amma tanacewa,

Ai aikin malam nakarangi yanakyau kiduba tun yarinyannan naarama danasa yatura mata aljani wadda ze hanata aure aizancen danake miki haryau bbu wanda yataba sallama da sunan yazo wajanta ga yan uwanta komai ya kankama biki kawae muke jira itakuwa shiru kikeji kamar an aiki bawa garinsu tana gama fadin haka suka tafa tareda shekewa da wata shedaniyar dariya aibata jira sunkara wata maganar dazata daga mata hankaliba tawuce jiri na ebar ta harshirin yasadda ita yakeyi

Tana shiga dakin mamansu kawae tafada kangado tasaki wani marayan kuka me tsuma ran me sauraro

Temakonta daya mama bata dakin yasa tayi kukanta mai isarta daganan tatashi tawanke idonta daganan taadauro alola tayi la'asar tayita addu'o in neman tsari daga sharrin mutum da aljani

Mamane itada inna kaltu mai aikinsu Zaune akicin tana dafawa baba ruwan shayi ni inna kaltu kuwa kinga diyarki tadawo daga makaranta

Najita shiru haryanxu batazo tacemin tadawoba inna kaltu take aikwa bangantaba inaga bata dawoba, to halan cewar mama dauke da gajeruwar damuwa aranta

Yarone dan kimanin shekaru 12 yayi sallama mama waekije inji baba yana falo yana jiranki toh kace masa ganinan zuwa

Fita tayi daukeda farantin ruwan shayi ahannunta tanufi falo anan tatarar da baba yana karanta jarida sallamarta ce tasashi ajiyewa tareda zare gilashin dake idonsa amsa sallamar yayi sannan takaraso ciki   tazauna tazuba ruwan shayin tamika masa yakarba yadan kurba sannan yayi gyaran murya mama tajuya ta fuskanceshi dan da'alama maganar dayakesonyi mai mahimmanci ne

Shin waini halima meyake damun diyarkine gabaki daya ina lura da ita kwanannan batasakewa batada walwala shin meke damunta?? Hmm wani gauron numfashi taja wallahi alhaji nima kwanakinannan haka nake kallonta narasa meke damunta nifa alhaji inaji yarinyar nan dagaske fadan mutanenne halan aljanine ya aureta

Kul karnasake jin wannan zance abakinki baba yayi saurin gargadarta ni inaji aji kina wani alkhairi ne yake BIBIYAR RAYUWARTA kace mahaifiyarta keyakamata kije kiji damuwarta

Bayan ta idarda sallah ne taki shingida tafara gyangyadi tagakamar inuwar mutum akanta agigice tafarka ta............

Shin wae wayake BIBIYAR rayuwar *hanna*??????????

Shin wae Su wayannnan mutane dasuke BIBIYAR yaruwarta ta suwayene???????

Shin dagaske Aljanin da aka turo mata ya sameta kuwa ko akwae wani boyayyen al'amari ne

Domin samun amsar wannan tambayoyi kubiyoni musamosu tare

Ur's
     Z33yyb3rw3r

Yanda Kaunata Da Adam Zango Tasa Na Baro Iyayena Na Taho Ganinsa - InJi Amina Amal


A cikin wata fira da jarumar nan ta wasan fim din Hausa mai suna Amina Muhammad da ake yi wa lakani da Amal ta yi da 'yan jarida, ta zayyana tiryan-tiryan yadda matukar kauna ta sa ta baro iyayen ta a kasar Kamaru ta taho Kaduna ganin Adam A. Zango.

Jarumar da ta bayyana cewa an haife ta ta kuma yi dukkan rayuwar ta har girmanta a kasar Kamaru, ta bayyana cewa jarumin da take matukar kauna duk a cikin 'yan fim shine Adam A. Zangon da ta ce shine ma musabbabin baro iyayen nata don dai kawai ta yi ido biyu da shi.

HausaMin.com dai ta samu cewa a cikin firar, Amal ta bayyana yadda tayi ta dauki ba dadi da iyayenta kafin su amince su barta ta taho wurin jarumin inda ta ce daga baya dai dole suka kyale ta saboda sun ga shine babban burin ta a rayuwa.

Haka ma dai jarumar ta bayyana cewa babban dalilin da yasa ta fara fim kuwa shine saboda ta tabbatarwa da kawayen ta da ma dukkan wanda ya santa cewar tabbas ta hadu da jarumin.

Thursday, 26 October 2017

Jaruma Nafisa Abdullahi Tace Ta Gaji da 'Yan Najeriya


Fitacciyar jarumar nan ta wasan fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood watau Nafisa Abdullahi ta fada a shafin ta na sada zumunta cewa ita ta gaji da 'yan Najeriya saboda sabar sa ido da ke gare su tare da kuma maida karamar magana ta zama babba.

Jarumar dai da yi wannan rubutu ne a shafin nata inda take nuna rashin jin dadin ta game da yadda wasu 'yan Najeriya ba su da wani aikin yi sai dai su zauna suyi ta ruruta maganar da bata kai ta kawo ba.

HausaMini.com ta samu dai jarumar haka ma dai bada shawarar cewa kamata yayi mutum yayi kokari ya gyara nasa kuskuren ba wai yayi ta ruruta na wani ba kamr shi baya yi.

Ga dai gundarin abun da jarumar ta rubuta: "Mutane da yawa ba aikin yi, shi yasa duk kankancin abu sai ya zama abun magana. Na gaji da yan Nigeria wallahi; kowa sai ya dinga yi kaman wani mutumin Allah mutumin Allah. Mutum ya yi kokari ya gyara kurakurensa, ya daina yi kaman shi waliyyi ne."

Friday, 17 February 2017

Yanda Ake Magance Matsalar "App Not Installed" A Wayar Andriod


Wani Abu Mafi Bacin Rai A Wayar Andriod Shine Yayin Da Kazo Installing Wani Application Musanman Ma App Din Mai Muhimmanci, sai Kaga Ya Nuna MaKa "App Not Installed" Ya KakanJi AranKa Yayin Da WayarKa Ta Nunama Wannan SaKon, Ba Dadi Koh ???




Za,a Iya Magance Wannan Matsalar Wata Kila Wayar TaKa Ko Anyi Rooting Dinta Ko Kuma Ba,ayi Rooting Dinta Ba,

Wasu Dalilai Ne Ke Haddasa Wannan Matsalar ??

Currupted App: Zai Iya Yiwuwa App Din Da Kake Son Install Dinsa Baya Da Kyau Wato Yayi Currupted, Toh Katabbatar App Din Da ZaKayi Amfani Dashi Kayarda Da Kyau Da Kuma InganCin Inda Kayi Downloading Dinsa.

Not Enought Space: Wannan Shine Kaso 80% Cikin 100 % Dake Jawo Matsalar "App Not Installed".

Unsigned Apk Installation: Idan WayarKa Version 2. Ko 3. 4.2 Ko 4.1 Ne Akwai App Da Idan Daga 4.4 Bane Bazai Taba Bude MaKa Ba Wannan Ma Itama Hanyace Babba Da Takesa Inkazo Install Din App Yace MaKa "App Not Install".

App Installation Location: Akwai Wasu Apps Din Da Su Suna Bukatar Kayi Install Dinsu A Kan WayarKa Ne .. Wasu Kuma Suna So Kayi Install Dinsu A Cikin SD Card DinKa Ne, Wato Memory Card Din WayarKa.

Tunda Yanzun Mun Fahimci Dalilan Dake Jawo Matsalar "App Not Install X" Yanzun Zamuyi Duba I Zuwa Ga Hanyar Da Zakabi WaJen Magance Matsalar,

  • Ka Tabbabar App Din Da Ka Samo Wata Kila Kayi Downloads A Cikin Wayar Taka Ya Kammala Downloads Ko Kuma Inma An Tura MaKa App Dinne To Ka Tabbatar AnKammala TuramaKa Shi.

  • Kamar Dai Yanda Na Fadi A Baya Wasu Application Din SuKan Zabi Inda Suke So Ayi Install Dinsu To Kawai Kayi Setting Install Location Ka Barshi A Automatic

  • Tunda Not Enought Space Shima Babban Hanyace DaKe Bada Gudunmawa WaJen Bada Matsalar "App Not Install X".

  • Wasu Kuma Apps Din Suna Da Bukatar Saikayi Reboot Din Waya Kafin Yayi Install.    

  • Daga Karshe Idan Kabi Duk WannanHanyar Bai Maka Aikiba Waton Bata Daina Nuna "App Not Install X" Kayi Kayi BacKup Din Kayayyakin 
  • Wayar Taka Kayi Wiping Dinta InshaAllah Komai Zai Dawo Dai Dai,


Wannan Shine Hanyan Bi Idan WayarKa Tana Nunama "App Not Install" Dafatan An Fahimta

Friday, 10 February 2017

Yanda Zaka Gano WayarKa Ta Andriod Bayan Ta Bata Ko Ansaceta Ta Hanyar Amfani Da Anriod Device Manager.

Kataba Asarar WayarKa, Ta Hanyar Saceta Ko Kuma Ta Fadi ?? Batare Daka Taba Samata Wani Software Da Ake Amfani Dashi Wajen Gano Waya Bayan Ta Bata Ba??



Ka Duba Wannan Post Din Domin Zai Iya Taimaka Wa Wajen Gano Ko Samo Batacciyar Ko Satacciyar WayarKa Ta Andriod,

Akwai Applications Da Dama Da Ake Amfani Dasu Wajen Gano Batacciya Ko Satacciyar Wayar Andriod .. Amma Sai Dai Mutane Da Dama Kan Iya Tunawa Dasu Ne Bayan Mai Faruwa Ta Faru .. Wata Kila An Sace Ko Ta Fadi ..

Hakan Na Nufin Kayi Latti Wajen Iya Ceto Ko Gano Wayar TaKa ..

Amma Hakan Ba Yana Nufin Cewa Kayi Hasarar Wayar Taka Bane . Ah'a

Akwai Hanyoyin Da Zakabi Domin Iya Ganowa, Batare Daka SaI Kayi Installing Din Wani Application Ba Kafin Batanta.

Yanda Ake Gano Wayar Idan Ta Bata Ko Ansace

Baramu Duba Gami Da Bayanai Akan Hanyoyin Da Zakabi

Hanya Ta FarKo Itace

1, Yanda Zaka Gano WayarKa Ta Andriod Ta Hanyar Amfani Da ANDRIOD DEVICE MANAGER, (ADM)

Abubuwan Da Ake Bukata ..

  • Dole Ya Kasance Wayar Taka Ka Taba Log In Din Google Account DinKa, (Gmail Account). 
  • Dole Wayar Takasance DATA Connection, Dinta Yana Bude Koda Da Cewa Ba Asalin SIM Card DinKa Bane A Cikinta. 
  • Dole Yakasance Ka Taba Bama Andriod Device Manager DinKa Dama Domin Gano Location, [Yana Cikin Settings Din Andriod Device Manager DinKa],


(Yana Cikin Settings Din Andriod Device Manager DinKa)

Andriod Devicte Manager-: Abu Ne Mai Saukin Amfani Wajen Gano WayarKa Idan Ta Fadi, Wani Abu Mai Dadi Shine ..

Bawai SaikaJe Kayi Install Na Wani Application Ba Wajen Gano WayarKa Idan Ta Bace, Kawai Abun Da Ake Bukata Shine Yakasance Wayar Taka Ka Taba Connecting Dinta Da Google Account DinKa, Sannan Kuma Data Din Wayar Yana Bude,

Kawai Abun Da Ake Bukata Ka Bude Andriod Device Manager DinKa Dake A Cikin Google Account DinKa, [Ta Cikin Brawser Kamar Google Chrome, Mozilla Fire Fox] Da Zarar Yayi Loading Zaiyi Kokarin Ya Gano Inda Wayar Taka Take,

Zai Nunama Map Din Inda Wayar Take Da Model Dinta (Sunanta) Sannan Zata Nunama Wasu Options, Kamar Su



  • Ring
  • Set up Lock & Erase





Idan Wayar Taka Ta Bata ... Zaka Sami Kamar Wayar Abokinkane Saikayi Wannan Aikin Da Ita [Wato Kayi Log In Din Email Din Dake A Cikin Wayar Da AKa Sace Ko Ta Bata] , Sannan Ana Iya Downloads Nashi Andriod Device Manager Daga Nan

Andriod Device Manager.apk

Andriod Device Manager Domin Saukaka Aikin Naka,

Idan Kaga Angwada Wannan Baiyi Ba .. Toh Zai Iya Yiwuwa Barawon Wayar Ya Cire Google Account Dinka A Cikin Wayar Kenan ..

Hakan Na Nuni Da Cewa Ba Wata Sauran Hanyar Da Zakabi Wajen Iya Gano Wayar Taka Data Bace (A Fahimtata)

Wednesday, 8 February 2017

COMEDY: BUSHKIDDO MazaJe Ne Epsd1 & 2



Comedy Din BushKiddo Yanda Ya Fito A Matsayin Kaura Tare Da Abokansa...


A Maimakon Su Nufi DaJi Sai Kawai Su Kare Akan Mai Saida RaKe

Asha Kallo Lafiya

BUSH KIDDO MaZaJe Ne Eps 1

DOWNLOAD NOW

BUSH KIDDO MaZaJe Ne Eps 1

DOWNLOAD NOW


Sunday, 5 February 2017

Ya Zanma Wayata Tana Yawan Mutuwa Ta Kunna Kanta Idan Ina Amfani Da Ita ??

Da Yawa Zakaga Kana Amfani Da Waya Ba Tare Da Ka Sani Ba Kawai Sai Kaga Ta Dauke Da Kanta, Sai Kuma Ta Kunna Kanta Can Kana Amfani Da Ita Kuma Sai Kaga Hakan Ya Sake Faruwa, Batare Da Kasan Kome Ya Haddasa Mata Wannan Matsalar Ba ...

Akwai Dalilai Da Dama Dakesa Hakan Na Faruwa, Ga Wasu Dalilan Kamar HaKa ... .

Storege Din Wayar Ko Yayi Currepted Ko Kuma Yayi Damaged

Kila Ka Antaba Saka Mata ROM Wajen Sawa Andan Sami Matsala

Kila Ruwa Ya Taba Shiga Wayar Ko Ta Fada Cikin Ruwan

Ko Kuma Ka Sa Mata Wani Gurbayaccen Appliation Din Dake Haddasa Mata Wannan Matsalar

Ta YaYa Zan Iya Kawar Da Matsalar ??

1, Ka Shigar Da Wayar Taka A Safe Mode:

Ya Akesa Safe Mode Din???

Kawai Ka Danne Bottom Din Kunna Wayar Taka Ta Andriod .. Na Dan Wasu Sakwanni, Har Sai Kaga Ta Nunama Wani Rubutu Kamar HaKa.



2, Saika Shiga Ka Goge Applications Din Daka Mata Installing Na Baya Baya (Wato Application Din Daka Sa Kafin Ta Fara Mutuwa Da Kanta) Domin Gogewa SaiKa Shiga

Settings>>Apps>>Downloaded Nan SaiKa Duba Wanda Kasa Kayi Uninstall Dinsu Anan

3, Ka Turning Off Na Auto Sync

Bude Settings, Ka Danna Kasa Zakaga “Accounts and Sync” SaiKa Taba Sashi A Off,, Sannan InKayi Update Din Google PlayStore SaiKayi Uninstall Din Updated Din,

Ya Zanyi Idan Nagama Bin Duk Wadannan Matakan Kuma Wayata Bata Daina Daukewa Ba ??

Kawai Abin Yi Shine Kayi Factory Reset, Zaifi A GareKa,

Dominyin Factory Reset Saika Taba Settings >> Backup & Reset>> Factory Data Reset

Taya Ake Fita Daga Safe Mode, ???

Kawai Ka Danne Power Bottom Din Wayar Taka, Wato Makunni Na Dan Wasu Dakiku, Saika Taba Reboot, Tana Kammala Reboot Daganan Ta Fita Daga Safe Mode

Friday, 3 February 2017

MTN Sun Fara Cerar Kudi Idan Kama Wani Transfer Din Kati, Ko Meyasa HaKa?




A Yayin Da MTN Suka Kaddamar Da Tsarin Nan Na Siya Da Siyar Wa Wato Share N Sell, Masu Hulda Dasu SunJi Dadi Sosai Tare Da Yaba Musu Akan Aikinsu, Haka Zalika Tun Lokacin Mutane Na Amfani Da Tsarin Daidai Yanda Yakamata Ba Tare Da Wani Tangarda Ba,



Duba Da Yanayin Matslar Faduwar DaraJan Kudi, Yasa MTN Suka Sa Tara Ga Duk Wani Mutum Da Zaiyi TransFer Din Kudi Daga Customer Zuwa Custumer,

Kamar Yanda Wani Ke Fadamin Cewa.

Yanzun Idan Yayi Transfer Daga Naira Hamsin #50 Zuwa Sama Kamar Dari Biyar Suna Cajansa Naira Daya Ne #1, Daga Dari Biyarr Zuwa Sama Nanma CaJinshi Daban, Cajin Da Zasumaka Ya Danganta Ne Da Yanayin Yawan Kudin Da Za,a

Daga Ranar 31 Ga Watan 1 Shekara 2017 Wannan Tsarin Ya Fara Aiki,

Don Haka Sai A Kula .. Yanzun Yin Transfer Sai Sun CaJe Ka Tukunna

Friday, 27 January 2017

Ba Satar Fasahar Fin Din India Na Yi Ba A Fim Din UMAR SANDA - Kamal Alkali



Fim din Umar Sanda ya fuskanci kalubale da dama daga al’umma akan cewar ya saci fim din ne daga fim din India, ba tare da la’akari da cewar hakan ya hallarta ba Inji Mai Bada Umarni Kamal Alkali.
Jigon labari akan wata yarinya da za’a yi wa fyade Allah ya bata sa’a har akayi rashin sa’a mai fyaden ya fadi ya mutu, na nuni ne da yadda mace zata kare kanta idan ta sami kanta a yanayin fyade makamacin wanna.
Kamal Alkali, ya ce ya dauki wani fim ne na India sakamakon labarin fim din ya zo daidai da irin labarin da yake son fitarwa a wannan lokaci wanda ya danganci fyade, ko da yake ya bayyana cewa zamani ya zo da babu laifin idan ka dauki labari daga wani fim ka wallafi shi a naka harshen matuka zaka bayyana a farko fim din cewa ga daga inda ka samo labarin.
Mai bada umurnin ya kara da cewa kamar yadda shugabanni ke ta kokarin cewar mutane su rungumi dabi’unmu na gari, bai ga laifi a fito da harkar fyade a fim ba kasancewa a yanzu haka dabi’ar da ke ciwa mutane tuwo a kwarya Kenan, kuma ko da ake cewa ya sata daga wani fim ai suma Indiyawa daga wani littafi na kasar China suka dauka.
Daga karshe ya kalubalanci mutane da cewar da ba’a fassara wannan fim na India a harshen Hausa ba, lailai da bazasu fahimci cewar ya kwaikwayi fim din India ba.
Ya kara da cewa abin sha’awa ne yadda mata jarumai idan sun shiga al’umma sai a baibayesu ana ta nuna musu kauna amma da zarar basa wajen kuma sai labarin ya sha banbam.

Saturday, 21 January 2017

Yanda Zakayi Amfani Da SunanKa Ko Sunan Wata A Matsayin MTN Caller Tunes DinKa, ..

Katabasa Caller Tunes A WayarKa ?? Nasan Koda Baka Taba Sawa Ba Ko Kuma Baka Taba Sha,awar MTN Caller Tunes Ba Zaka Iya Sha,awar Wannan Salon Caller Tunes Din ..





Kamar Dai Yanda Kowa Ya Sani Caller Tunes Wata Wakace Da Wanda Ya Kira WayarKa Zai Jita, Wakar Ta Iya Zama Wacce Yakeso Ne Ko Kuma Wanda Su Sukaga Dama Su Sakama Wakar Dasuga Dama

Wannan Zaka Zabi Sunan Da Kake Bukatane A Matsayin Wakarnan Da Za,a Dunga Saurare Yayin Da Aka KiraKa ... Za,a Saurari Waka Ce Da SunanKa Ko Sunan MasoyiyarKa Tare Da Kirari .

Idan An Fahimci Abun Da Nake Nufi Sai Inci Gaba

Da FarKo Kawai Ka Shiga Wajen Text Message DinKa .. Ka Tura Text Din SunanKa Ko Sunan Da Kakeso A Sa A Matsayin Caller Tunes Dinka ..

Misali : Ubablog To 441 Da Zarar Ka Tura Saika, Zasu Turama Text

Kamar Haka

The ReQuest Has Been Accepted. You Will Get A Call Within A While,

To Inkaga Wannan Text Din Yana Nuna Cewa Akwai SunanKa Kenan

Idan Kuma Kaga Haka

Your ReQuest For ...... Has Been Received And Will Be Processed ..

Hakan Na Nufin Ba Sunan Ka Cikin Na,urar Tasu ..

Bayan Sun Turama Text Zakaji Kira Daga 441 , Idan Ka Dauka Zau Fara Magana Suna Fadama Yanda Abun Yake .. Waton Zasu Nunama Ka Danna Numba 1, Domin Saka Wakar Da KaJi A Matsayin Caller Tunes Din Naka, Ka Dannan Numba 2, Domin Turamma Aboki Ko Budurwa, A Matsayin Caller Tunes .. Bayan Sun Kammala Fadan Wannan Abubuwan ZakaJi Sun Sakama Wakokin Da Zaka Zaba ..

Idan Sun Sakama Waka Kaji Bata Maka Ba .. Saika Danna 4, Domin Jin Wasu Wakokin; Idan Kaji Wacce Tamaka Saika Danna 1, Zasuyi Magana Cewa Kadan Jira Kadan Domin Kammala Downloads Na Caller Tunes Din, Zasuce Press 1 To Comfirm Sai Kuma Ka Sake Danna 1, Daganan Zasuce Successfully,

Daganan Da Zarar An KiraKa Za,aJi WaKane Dare Da Taken SunanKa Na Tashi ..

Monday, 26 December 2016

Yanda Zaka Dawo Da Hotuna, Videos, WaKoki, Tare Da Documents DinKa, Daga Cikin Memory Card Din Daya Lalace,

Ka Taba Sa HotunanKa Da KakeJi Dasu,Vidioes,WaKoKi Tare Da Wasu Muhimman TaKardunKa A Cikin Memory Card DinKa, Daga Baya Aka Sami Akasi Memory Card Din Yazo Ya Lalace??

Ya Kaji A Lokacin ?? Ba Dadi Ko? HaKa Abun YaKe, Wani Ma Kam SaiyaJi Kamar Yayi Ciwo, A Yayin Da Memory Card Dinsa Ya Lalace, Idan Ya Tuna Da Hotunan Sa, Domin WaKa, Videos, Duk Zai Iya Samun Wasu .. Amma Hoto Kam Ya Tafi Kenan,

Idan Ka/Kina Daya Daga Cikin Wanda Haka Ta Faru Dasu, Biyoni Kaga Yanda Zaka Iya Dawo Da Komai Na Memory Card DinKa, Ba Tare Da Bata Lokaci Ko Wani Wahala Ba, Koda Ko Memory Card Din Ya Lalace Ne Waton Yana Nunama "SD Card Damaged"

Abubuwan BuKata

1, Lalataccen Memory Card; Yi Maza Ka Dakko Lalataccen Memory Card DinKa, (Ka Shareshi Domin Kila Ya Dade A Ajiye Ya Kwashi Qura)

2, Ka SauKar (Downloads) Na Wannan Software Din Remo SD Card Recover For Andriod.exe 

3, SaiKayi Install Dinsa A Cikin Computer,

SaiKa Bude Shi Software Din DaKayi Download Dinsa Wato Remo Recover For Andriod,

Zai Nunama HaKa




Saika Taba Alaman Green Dinnan

Zakaga Ya Nunama Setting Up Connection (Alamun Yana Loading Kenan)



SaiKasa Memory Card Din A Cikin Wayar Andriod, Bayan Kasa SaiKayi Connecting Din Wayar Da Memory Card Din Ke Ciki Da Computer Din, (Ka Tabbata Yayi Connect Wayar Da Computer Din)


Zai Fara Loading

Daganan Zai Nunoma Wani Dan Alama, Da Suna DisK 1 Kamar Haka,



SaiKa Tabashi, Idan Ya Nunama Alamar Kamar Ka Zaba, SaiKa Je Kasan Software Din Ka Taba Dan Karamin Arrow Dinnan Wato Next Kenan,




Daganan Zai KaiKa Inda Zaka Zabi Jerin Abubuwan Da Kakeso Ka Dawo Dasu, Idan Kanaso Ka Dawo Da Komai Ne Sai Kayi MarK All



Bayan Ka Zaba Saika Sake Taba Alamar Arrow Dinnan Na Kasa Wato Next,




Zai Nunama Loading Yana Cewa Searching Lost Data



Yana Kammalawa Zai Nunama Wani Imformation SaiKa Taba OK,



Zai Cema Ka Zabi Abun Da Kakeso Ka Dawo Dashi, Anan Ma SaiKa Sake MarK All,



[Kafin Ka Dawo Dasu Zaka Iya Preview Kaga Komai NaKa]

Zai Sake Nunama Wani Imformation Din, SaiKa Taba Ok



SaiKa Taba Dan Karamin Arrow Dinnan Na Kasa,

Yana Wucewa Zai Nunama Cewa Ka Zabi Inda Kakeso Kayi Saving Din KayayyakinKa Wato (Hotuna,Videos,Musics) Da Kakeson Dawo Dasu,



Saboda Gudun Matsala, SaiKa Creat New Folder, Ka Samasa Suna, Zaka Iya Samasa Suna Recover Files, Ko Ka Zabi Wata Folder din Da Kasan Bakomai Layi Saving Cikinsu

SaiKa Shiga Ka Zabi Folder Din Recorver ZaiKa Saika Taba OK,


SaiKa Taba Karamin Arrow Next



Daganan Zai Fara Saving Ma KayayyaKinKa

Zai Nunama Saving Data To .......?



Yana Kammalawa Zai Sake Nunama Wani Imformation Din SaiKa Taba OK



Zai Nunoma Folders Tare Da Yawan Files Din Dakayi Nasarar Dawo Dasu

Kamar HaKa,



SHIKENaN!

BaYani : Idan Kaga BaiMaka Ba Ka Sake Bin Bayanin Namu A HanKali InshaAllah ZaKa Fahimta

Saturday, 24 December 2016

Yanda Ake Gyara Memory Card Ko Flash DinKa Idan Ya Lalace Yayi (Currupt)





Memory Card Shine Abu Na Biyu Mafi Soyuwa Da Muhimmanci A Cikin Waya Bayan Sim Card,

MukanJi Ba Dadi Yayin Da Memory Card Dinmu Ya Lalace (Currupted)

Misali Kana Kan Amfani Da Memory Card DinKa, Kwatsam Sai Kaga Ya Nunama "Damaged SD Card" InKayi Format Din A Cikin Wayar Yakiyi, Inma Ansa A Computer Anyi Format Dinsa Haka Zai Ta Nuna Maka Koda Kayi Format Din Bazai Ci Gaba Da Amfaniba Kuma ...




A Takaice Dai Memory Card DinKa Ya Lalace Ka Rasa Komai Na Cikinsa, Ka Rasa Shi Kansa Memory Card Din

Abin Da Zamuyi Magana A Yau Shine Yanda Zaka Gyara Memory Card DinKa A SauKake Ba Tare Da Kayi Amfani Da Wani Software Ba .....

Abubuwan Da Ake BuKata Kafin Gyara Memory Card Ko Flash,...

1, Natsuwa .. Yana Dakyau Ka Natsu Sosai WaJen Gyara Lalataccen Memory Card Ko Flash DinKa,

2, Lalataccen Memory Card, Tare Da Card Reader, Waton Gidan Sa Memory Card Din

3, Computer, Dole Da Ita ZaKayi Aikin WaJen Gyara Memory Card Din NaKa .

Da FarKo Ka Bude Coputer Din SaiKa Danna Alamar Windows Din Computer Din,



Zai Fitoma Da ShafuKan Computer Din A Kasa Akwai WaJen Search Sai Ka Rubuta "CMD" Kana Ruburawa Zakaga Ya Fito, SaiKa Budeshi

Inya Bude SaiKa Rubuta DISKPART SaiKa Taba Enter Key Na Computer Din

Daganan Zai KaiKa Wani Shafin, Sai Ka Rubuta “LIST DISK SaiKa Danna Enter Key

Zai Nunoma DisK Wato Memory Din Computer Din Da Kuma Lalataccen Da Kasa ... Sai Ka Duba Kaga Wannene Lalataccen A Ciki, Disk 1 Ne Ko DisK 2, Amma Yawanci Yafi Zuwa A DisK 1,

Sai Ka Rubuta “SELECT DISK 1” Sai Ka Taba Enter Key

Zai Nunama

DISKPART> DisK 1 Is Now Selected

Sai Ka Sake Rubuta “CLEAN” SaiKa Taba Enter Key

DisKPart> Succeed Cleaning The Disk.

Saika Sake Rubuta “CREATE PARTITION PRIMARY” Sai Ka Taba Enter Key, Zai Nunoma

DISKPART> Succeed Creating In The Specified Partition

Sai Ka Rubuta “ACTIVE”

SaiKa Taba Enter Key

Zai Nunoma

DISKPART> Marked The Current Partition As Active

SaiKa Rubuta “SELECT PARTITION 1” SaiKa Taba Enter Key

Zai Nunama, Partition 1 Is Now The Selected Partition

Sai Ka Sake Rubuta “FORMAT FS=FAT32” SaiKa Taba Enter Key

Daganan Zai Fara Format Zakaga Yasama 0% To Complete, A Haka A HanKali Har Sai YaKai 100 %

Ka Tabbatar Kayishi Kamar Yanda Yake A Wannan Hoto




YaKan Dau Lokaci Kafin Ya Gama Gyaruwa

BaYani

 Na Gwada Na TabbataR Da Ingancinsa, Idan Ka Gwada BaimaKa Aiki Ba, Ka Min Magana Ta WhatsApp 08169025912

Sunday, 16 October 2016

Yanda Zakayi Blocking Na Wani Website A Cikin Wayarka Ta Andriod





Kila Ko Kanaso Kadakatar Da Wani Daga Budemaka Wayarka Yana Shiga Shafukan Da Basu Dace Ba, 

Ko Kila Kai Kanka Akwai Shafukan Da Kake Da Kudirin Son Daina Shigar Su Domin Rashin Dacewar Su, Amma Hakan Taci Tura, To Saika Jaraba Wannan Matakin Ta Cikin Wayar Taka Ta Andriod.

YANDA AKEYI

1]... Da Farko Kana Da Bukatar Wannan App DinHost Editor.Apk A Wayartaka Ta Andriod..

2],... Bayan Ka Kammala Install Dinsa, Saika Bude, Idan Ka Bude Saika Taba Kan "New Entry" Daga Menu Din App Din

3]... Saika Sa 127.0.0.1 A Wajen Ip Address

4]... Wajen Host Entries, Saikasa Sunan Website Din Da Zaka Yi Blocking Dinsa Misali Sino.Com Saika Taba Kan ‘Save New Host' Domin Yin Save Din File Din

                  Screenshot

Zaka Iya Blocking Din Website Da Dama Ta Wannan Hanyar, Idan Kayi Blocking Din Website Na Farko Da Wannan IP Din 127.0.0.1 To Website Na Biyu Saikasa IP Dinsa Kamar Haka 127.0.0.2 Na Uku Kuma Kamar Haka 127.0.0.3 Yana Nufi Kana Canja Numban Karshen Kenan,